Gwamantin Jihar Borno ta Haramta Siyar da Barasa a fadin Jihar.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin dakatar da sayar da Barasa da sauran kayan maye a birnin Maiduguri da kewaye, yana mai zargin wasu jami’an tsaro da hannu a yaduwar laifuka da munanan dabi’un a tsakanin al’umma.
Farfesa Zulum ya bayyana haka ne a jiya Talata, yayin kaddamar da kwamitin da aka sake wa fasali domin rushe otal-otal da gidajen karuwai da maboyar ’yan daba da masu aikata laifuka a fadar jihar da kewaye.
A cewar gwamnan, wasu tsofaffi da ma’aikatan jami’an tsaron da ke aiki a yanzu sun taka rawa matuka wajen jefa matasa cikin ayyukan laifi, irin su ta’addanci, karuwanci, shaye-shaye da kuma aikin daba.
Gwamna Zulum ya ce yawaitar sayar da barasa da kayan maye na kara haddasa rikici tsakanin kungiyoyin masu tayar da hankali, kawalci, da kuma satar mutane, wanda hakan ke kara barazana ga zaman lafiya jihar.