Al’ummar Kano na Cikin Ruɗani Bayan Naɗi Sarautar Galadima.

A yau Juma’a, an shiga ruɗani a masarautar Kano bayan da sarakuna biyu masu ikirarin sarautar Kano suka naɗa Galadima daga kowannensu.
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya jagoranci majalisarsa da hakimai da magoya bayansa wajen naɗa ɗan uwansa Sunusi Ado Bayero, a matsayin sabon Galadiman Kano.
A daya ɓangaren kuma, Sarkin Kano Muhammad Sunusi II, shima ya jagoranci tasa majalisa da hakiman da ke masa biyayya, inda ya naɗa Munir Sunusi, ɗan uwan mahaifinsa, a matsayin Galadiman Kano.
Wannan rikici ya samo asali ne bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, wanda ya bar gurbi a daya daga cikin muƙaman sarauta mafi ƙima a masarautar.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya halarci nadin da Sarki Sunusi II ya gudanar a fadar masarautar da ke Kofar Kudu, yayin da magoya bayan jam’iyyar APC suka halarci naɗin da Sarki Aminu Ado Bayero ya yi a fadar Nasarawa.Yanzu haka, masarautar Kano na fuskantar rikici mai zurfi, yayin da ake ci gaba da tambaya: wa ne Galadiman Kano na gaskiya.