Gwamna Fubara ya Nemi Afuwar Wike.

A cikin babin rikicin siyasa da ke faruwa a Jihar Rivers, an ruwaito cewa Gwamna Siminalayi Fubara, wanda aka dakatar, ya ziyarci Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, a gidansa da ke Abuja, inda ya nemi afuwar sa tare da neman yin sulhu.
Jaridar PREMIUM TIMES, ta ruwaito cewa an kai Fubara gidan Wike ne a ranar Juma’a, 18 ga Watan Afrilu, ta hannun Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da tsohon gwamnan jihar, Olusegun Osoba. Wata majiya ta bayyana cewa Fubara ya durƙusa, ya riƙe ƙafafun Wike yana roƙon sa gafara da kalmar, “Oga na, don Allah ka yafe mini.
”Wannan ganawar ta biyo bayan wani rahoto da ke cewa Fubara ya je Landan domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da rikicinsa da Wike. Tinubu daga baya ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Rivers tare da dakatar da Fubara da wasu ƴan siyasa da aka zaɓa na tsawon watanni shida.
Majiyoyi sun bayyana cewa an umarci Fubara da ya koma Rivers domin ya bayyana wa magoya bayansa da dattawan jihar halin da ake ciki.Mai magana da yawun Wike, Lere Olayinka, ya tabbatar da ganawar amma bai bayar da cikakken bayani ba a dan gana da ganawar ta su ba.