Labarai
Mataimakin Gwamna ya koma Siyar da Itace.

Caleb Amaswache wanda tsohon Matemakin gwamna a jihar Vihiga dake kasar Kenya ya koma siyar da itacen girki bayan saukarsa daga mulki a shekarar 2017.

An rawaito cewa Caleb ba barawon shugaba bane kamar sauran shugabannin kasar ta Kenya ya tsaya ne a iya albashinsa Ksh600,000 duk wata bai yadda da daukar kudaden jiharsu ba.
Duk da cewa Caleb ya kasance maiyawan shan giya wacce ita ce ta cinye masa mafi yawa daga albashinsa, bayan da yaga kudi sun kusa kare masa sai kawai ya yanke shawarar fara siyar da itace a kofar gidansa.