Labarai
Hisbah ta Haramta Sauraro Waƙar Hamisu Breaker.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi kira ga matasa su ƙauracewa sauraron waƙar Amanata ta Hamisu Breaker.Mataimakiyar Babban Kwamandan Hisbah ɓangaren mata Dr. Khadija Sagir ta bayyana hakan.

Dr. Khadija ta ce, waƙar ta fito ƙarara tana nuna zina daga yadda mata suke hawa suna wani lanƙwashe-lanƙwashe da karya murya a manjar sadarwa ta TikTok.A ƙarshe ta ce, wannan waƙa haramun ce bakiɗayan ta.