Siyasa
Shugaban Kasa ba Shi da Hurimin Korar Gwamna da Aka Zaba – Femi Falana

Shahararren lauya nan kuma mai rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana (SAN), ya bayyana a shekarar 2013 cewa babu wata doka a kundin tsarin mulkin Najeriya da ke bai wa Shugaban Kasa damar sauke gwamna da aka zaba ta hanyoyin dimokuradiyya.
Falana ya jaddada cewa shugabanci a Najeriya na bisa ka’idojin tsarin dimokuradiyya, don haka babu wata doka da ke bai wa shugaban kasa iko na tsige gwamna, komai irin yanayin da aka tsinci kai a ciki.
Wannan furuci na Falana na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan ‘yancin gwamnatocin jihohi da kuma iyakar ikon da shugaban ƙasa ke da shi kan shugabannin da aka zaba a matakin jihohin su.