Labarai
Gobara ta Tashi a kasuwar Ƴan Gwan-Gwan ta Kwalema Dake Kano.

Wata gobara da ta tashi a safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.
Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe wannan gobarar da ke neman wuce gona da iri.
Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu ba su gano musabbabin tashin wannan gobarar ba.