Siyasa

Sanya Dokar ta Ɓace a Jihar Rivers Tamkar Yaudara ce a Siyasance da Kuma Nuna Rashin Gaskiya Ƙarara – Atiku Abubakar

Cikin Wata sanarwar da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta na Facebook.Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban Najeriya a zaɓen da ya gabata Alhaji Atiku Abubakar.

Yace duk wanda ke bibiyar rikicin da ke faruwa zai fahimci cewa akwai sa hannun shugaban Tinubu a rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Rivers.

Ƙin yin wani abu don daƙile wannan rikici ko kuma ƙin yin hakan da gangan abin kunya ne matuƙa.Baya ga sa hannu a siyasar da ake yi a Rivers, taɓarɓarewar tsaro da ta kai ga lalata muhimman ababen more rayuwa na ƙasa abu ne da ya rataya a wuyan Shugaban Ƙasa.

Ya ƙara da cewa Tinubu ba zai iya kauce wa alhakin fitinar da gwamnatinsa ta bari ta faru ba ko kuma ta ƙarfafa.

Abin takaici ne yadda yankin Neja Delta ya koma zamanin tashin hankali da rashin zaman lafiya a ƙarƙashin kulawar shugaba Tinubu, inda ya rusa zaman lafiya da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya samar bayan yi aiki tukuru.

An wofantar Shekaru da wannan yanki yayi cikin zaman lafiya yayinda suke cigaba da ƙoƙarin cimma wata manufa tasu ta siyasa.Idan har an lalata ababen more rayuwar ƙasa a jihar Rivers, to Shugaban Ƙasa ne ke da alhakin hakan.

Hukunta al’ummar Jihar Rivers saboda rikicin mulki tsakanin gwamnan jihar da yaran fadar Tinubu, cin amanar dimokuraɗiyya ne kuma dole ne a la’anci hakan da kakkausar murya a cewar sa.

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button