Tinubu Uban Gida na ne, Manufofinsa na ke Suka ba Shi ba – Ali Ndume

Sanata, mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume yace girmamawar sa ga shugaban Tinubu a daidai lokacin da ya yi shura wajen sukar manufofin gwamnatin sa.
Da ya ke jawabi yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a cikin shirin ‘Politics Today’, Sanatan ya nuna da dangantakarsa da Tinubu tare da jaddada kudurin sa na yin suka mai ma’ana domin kawo cigaban a Najeriya.
“Ni ba na sukar gwamnati. Ita ce gwamnatinmu.
Shugaba Tinubu na daya daga cikin masu ba ni shawara,” in ji shi.
Da ya ke bayani kan hoton sa da Tinubu cikin nishadi da ya yadu a kafofin sadarwa, Ndume ya ce ya ce, “Ce min ya yi ba na zuwa Villa.
Na ce masa bai CD na zo ba ne shi ya sa, sai ya ce zan iya zuwa da daddare.
“Sai (Tinubu) ya ce min zai halarci daurin auren ƴa ta, duk da cewa ya zo daidai da ranar tunawa da tsoffin sojojin Najeriya.
Don haka bayan bikin, ina tsammanin zai tafi.
Ya ce ba zai je ko ina ba; cewa zai halarci daurin auren. Abin da ya faru ke nan.”