Yan Najeriya Kada ku Yankewa Kauna Daga Ƙasar ku – Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya Good luck Jonathan ya ce har yanzu akwai kyakyawar fatanci a nan gaba da take bukata ya tabbata, kamar yadda shugabannin farko suka yi wajen dasa tubalin ginin kasar.Yayin da yake tsokaci a kan bikin cikar Najeriya shekaru 64 na samun ‘yancin kai daga hannu Turawan mulkin mallaka, Jonathan ya ce a daidai lokacin da jama’ar Najeriya ke jinjinawa shugabannin farko, ya na da muhimmanci a mayar da hankali wajen bada gudumawa da ake bukata domin habaka kasar.Tsohon shugaban yace a karon farko an kwashe shekaru 25 ana gudanar da dimokiradiya ba tare da matsala ba, tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999, kuma matakin ya bada damar samun ci gaban tattalin arziki da hadin kan jama’a da kuma dorewar kasar a matsayin dunkulalliyar ƙasar.Jonathan ya kara da cewa duk da yake ana fuskantar wasu manyan kalubalen da suka hana kasar samun ci gaban da take bukata ta fuskar tsaro da tattalin arziki, ya na da matukar muhimmanci a karfafa hukumomin kasa wadanda za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro da kuma gudanar da sashishin zabe.Tsohon shugaban ya kuma bukaci masu rike da madafun iko da su tabbatar da gaskiya da adalci a kowanne mataki, musamman wajen raba mukamai da arzikin kasa, tare da bai wa matasa damar shiga a damawa da su.A karshe tsohon shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su kaucewa yankewa ƙasar kauna wajen tunanin cewar ba za’a iya shawo kan wadannan matsalolin da suka yi wa ƙasar katutu ba.