Labarai

Gwamnatin Najeriya ta Bada Umarnin a Buɗe Iyakokin Najeriya Da Nijar.

Gwamnatin ta ba da umarnin buɗe iyakokin kan tudu da na sama da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar tare da ɗage duk wasu takunkumai da aka ƙaƙaba wa kasar nan take.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Ajuri Ngelale ya fitar a yau.

Sanarwar ta ce wannan umarni ya dace da shawarar da Shugabannin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) suka yanke a babban taron da suka gudanar na musamman a ranar 24 ga Fabrairun wannan a Abuja.

Mista Ngelale ya kara da cewa shugabannin na ECOWAS wanda shugaba Tinubu ke jagoranta, sun kuma janye duk takunkuman da aka kakabawa Jamhuriyyar Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button