Siyasa

Gwamnatin Kano ta Dakatar da Masarautu Daga Nada Sababbin Mukamai.

Maaikatar kana nan hukumomin jihar Kano ce ta fitar da sanarwar, inda ta dakatar da masarautun daga gudanar da ko wane irin sabbin nade-naden mukamai.

Masarautun da abin ya shafa sun haɗa da masarautar Kano da Bichi da Rabo da Gaya da kuma Karaye.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da gwamnatin ta dakatar da gudanar da nadin wani hakimi a masarautar Bichi.

gwamnatin ta dakatar da nadin Salisu Ado Bayero wanda kane ne ga Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne Masarautar Bichi ta rubutawa Salisu Ado Bayero wasika inda ta sanar da shi amincewar sarkin na a nada shi a matsayin hakimin gundumar Bichi.

Wasikar ta umurci Yariman da ya zo fadar a ranar Juma’a 1 ga watan Maris domin yi masa rawani a matsayin hakimin gundumar.

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button