Labarai

Gobara ta tashi a Dakin Kwanan Dalibai Mata a Jami’ar Jihar Yobe.

An kwantar dalibai takwas a asibiti sakamakon gobara da ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Yobe da ke Damaturu.

Gobarar de ta tashi ne sanadiryar wata tukunyar gas din girke inda ta kone dakin kwanan daliban da misalin karfe 7 na daren jiya Talata.

Hukumomin jami’ar jihar sun ce ’yan kwana-kwana da na hukumar kashe gobara ta jihar ne suka shawo kan gobarar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Abdulmumini Kolo Gulani ta ce an kwashe dukkan daliban, ba sa samu asarar rai ba.

Ya kara da cewa ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, amma hukmomin jami’ar na aiki tare da sashin tsaro da kashe gobara na jami’ar domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Gwamna Mai Mala Buni na jihar ya jajantawa masu jami’ar da kuma daliban amma ya yi hamdala saboda ba a rasa rai ba.

Ya kuma umurci hukumar agajin gaggawa ta jihar da ta samar da abinci, tufafi, da shimfidu, a yayin da gwamnatin za ta sama wa daliban wani wurin kwanan.

Gwamnan ya bukaci daliban da al’ummar jihar da su yi taka tsantsan tare da kauce wa abubuwan da za su iya haddasa gobara a nan gaba.

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button