Za’a Gurfanar da Luis Rubiales a Gaban shari’a kan sumbatar Hermoso

Wani Alkalin ƙasar Sifaniya ya ce ya kamata tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar Luis Rubiales ya gurfana a gaban kotu kan sumbatar da ya yi wa kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafar matan ƙasar, Jenni Hermoso a gasar cin kofin duniya.
Mista Rubiales ya kama kan Ms Hermoso kuma ya sumbace ta yayin gabatar da jawabi bayan nasarar da Sifaniya ta samu a Australia.
Ta ce sumbatar “ba da amincewarta ba ne”, iƙirarin da Mista Rubiales ya musanta.
Alkalin ya ce ya gano wasu isassun shaidun da za su iya bayar da damar ci gaba da shari’a.
A yayin sauraren ƙarar da aka yi a Madrid, alƙalin ya bayyana sumbatar a matsayin “ba ba da amincewar juna ba kuma wani shiri ne mai ban mamaki”, a cewar wata sanarwa da kotun ta aike wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A baya dai masu gabatar da ƙara sun tuhumi Mista Rubiales da laifin yin lalata da kuma tilastawa.
Hukunce-hukuncen irin wannan sumbatar ya haɗu da tara da kuma shekara hudu a gidan yari.
Lamarin dai ya shafi shugabannin hukumar kwallon kafar Sifaniya da dama da suka hada da tsohon kocin Hermoso da tsohon manajan tallace-tallace da kuma daraktan wasanni na ƙungiyar maza.
Ana zargin Jorge Vilda, da Rubén Rivera da Albert Luque da tursasa Ms Hermoso wajen faɗin cewa da amincewarta ya sumbace ta.
Alkalin da ke birnin Madrid ya ce ya kamata su ma ‘yan wasan uku su gurfana gaban kotu.