Labarai

Rundunar Sojojin Najeriya Sun Kashe Gawurtaccen Dan Fashin Daji nan Janari.

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi ƙarin haske kan yadda ta ce dakarunta suka kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Janari, da mabiyansa da dama a wani sumame da suka kai ƙarƙarshin rundunar tabbatar da tsaro ta Operation WHIRL PUNCH.

Rundunar ta bayyana cewa ta yi nasarar kawar da ɗan bindigan ne yayin da ya ke tattara maƙarrabansa da niyyar kai hari a maɓoyarsu da ke ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna, a arewacin Najeriyar.

Kakakin rundunar, Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya shaida wa BBC cewa rundunar ta sami nasarar ne bayan ta ɗauki lokaci tana dakon gungun ‘yan bindigan kafin suka yi dace suka yi arangama da su a yankin Gadar Katako da ke ƙaramar hukumar Igabi.

‘Lamarin ya auku ne a ranar 18 ga watan Janairu, amma sai bayan ‘yan kwanaki muka sami tabbacin cewa an kashe wannan ɗan bindiga da mabiyansa. Shi wannan mutumin Janari mun sami labarin cewa yana da hannu cikin harin da aka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna’, kuma muna da tabbacin cewa yana da hannu a cikin hare-haren da ake kaiwa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.’ In ji shi.

Air Vice Marshal Gabkwet ya ƙara da cewa dangane da irin miyagun ayyukan da ‘yan bindiga irinsu Janari ke aikatawa akwai buƙatar a ɗauki tsauraran matakai a kansu a duk lokacin da dama ta samu.

Ya ce akwai buƙatar ganin cewa an sami haɗin kai daga duk ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki a harkar tsaro domin a samu damar magance matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Ya ƙara da cewa ‘Ita wannan harka ta ‘yan bibdiga, ba wai za ka ce idan ka kashe duka shugabanninsu shikenan abin ya ƙare ba, mu dai za mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu na soji, amma dole ne a magance matsalolin da ke bai wa waɗannan mutane damar jawo hankalin ƙananan yara da suke tattarawa cikin mabiyansu. Sojoji za su yi nasu, jama’a ma su yi nasu, da kuma gwamnati a kowa ne mataki.’

Ya yi bayanin cewa muddin ba a magance matsalilin da al’umma ke fama da su ba, kamar su rashin ilimi da rashin aikin yi da kuma samar da abubuwan more rayuwa ba to za a ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro saboda ko sojoji sun kashe waɗansu za a ci gaba da samun waɗanda za su maye gurbinsu a gungun ‘yan bindigan.

Ya ce: ‘Akwai buƙatar kowa ya bayar da tashi gudumawar don harkar tsaro ta kowa ce, dole ne mu haɗa hannu. A tarihi babu inda aka taɓa magance matsalar ta’addanci da bindiga kaɗai.’

Matsalar tsaro ta daɗe tana addabar arewacin Najeriya, musamman jihar Kaduna inda aka daɗe ana ɗauki-ba-daɗi da ‘yan bindiga a hanyar da ta tashi daga jihar zuwa Abuja babban birnin tarayyar ƙasar.

Duk da cewa dai a watannin baya wannan hanyar ta fara samun sauƙin wannan matsala, makonni biyu da suka gabata ‘yan bindiga sun tunatar da cewa akwai sauran rina a kaba inda suka kai hari tare da sace mutane a kan hanyar.

Duk da ɗan koma-bayan da aka samu, jami’an tsaron ƙasar sun bugi ƙirjin cewa a shirye suke don yaƙi da matsalar rashin tsaro a duk sassan ƙasar.

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button