Labarai
Wani Jariri Ya Ɓata a Wani a Asibitin a Kano

Wani Rahotanni sun bayyana cewa an rasa wani Jariri ‘dan kwana ɗaya da haihuwa a asibitin waziri gidado dake Kano.
Bayan Mahaifiyar yaron ta haifi yaron ta a gida a ranar Alhamis sai ta kamu da rashin lafiya inda a nan aka garzaya da ita asibitin domin kula da lafiyar ta.
Da misalin karfe 8 na dare tana cikin halin rashin lafiya matsananciya.
A nan wata mata ta dinga hilatar kakar wannan yaron har ta tafi da ‘dan nasu wanda kawo yanzu babu labarin sanin inda yake.
Saide Mahaifin yaron mai suna Aliyu yace ya tafi sallar ya bar mahifiyar yaron da kakar sa a asibiti sai da ya dawowa ake sanar dashi batan yaron nasa.