Siyasa

APC Ƙyanƙyasar PDP ce Don Haka ba ma Tsoranta – Sule Lamido.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa da arewacin Najeriya, kuma jigo a jam’iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban riƙon kwarya na jam’iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki ƴan Najeriya za su sake shiga ƙunci ba gaskiya ba ne.

Alhaji Sule Lamido ya ce duk ɗan APC da yake ganin PDP ce ta lalata Najeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali ɗan PDP ne.

Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala’ice, azaba ce, amma duk da hakan ayi masa afuwa saboda tsoho ne.
Ya ƙara da cewa;

“Amma kar ya manta kuma ƴan Najeriya kar su manta zaɓukan da aka yi a Najeriya na shekarun 1999 da 2003 da 2007 da 2011 kuri’un PDP kaɗai sun fi na dukkan jam’iyyu.

Saboda haka, duk dabarar mai dabara, duk wayo mai wayo, sai da aka samu mutanen PDP, da Olusegun Obasanjo a lokacin suna fada da Goodluck Jonathan, da su Bukola Saraki, Atiku da Abdullahi Adamu da Aminu Waziri Tambuwal da sauran gwamnonin PDPn , suka marawa APC baya aka haifi ainahin gwamnatin Buhari.

“Abin da Bisi ya manta shi ne gwamnatin Buhari ƴar haramun din PDP ce, yar PDP ce amma ta haramtacciya.”

Majiya: Bbc Hausa

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button