Wasanni

Baturen Ɗan Dambe ya sha Kashi a hannun Shagon Yellow Ɗan Zuru.

An gudanar da wasan Dambe a gidan Dr. Mamman Shata Theatre dake Katsina, inda a lokacin Damben wani baturen Ɗandambe yasha kashi a wajen baƙar fata Shagon Yellow Ɗanzuru a Katsina.

Shagon Yellow Ɗanzuru ya wahalar da baturen Ɗandambe matuƙa, inda nan da nan aka raba damben ganin yadda yayi masa jina-jina don karta kai ga kisa, inda a lokacin alƙalin wasa ya tsaida wasan. Jim kaɗan bada jimawa ba, da alƙalan wasa suka duba maki Shagon Yellow Ɗanzuru shi ne yayi nasara akan baturen Ɗandambe.

Tunda farko, an buɗe kakar wasan damben na shekarar Dubu Biyu da Ashirin da Huɗu a ranar 13 ga watan Janairu 2024. Inda duk waɗanda suka samu nasara a wasan duk yawancinsu ‘Yan Arewa ne.

Kamar yanda jaridar Katsina Post ta rawaito, wasan damben yayi daɗi sosai inda mutane da dama ne suka cika gidan wasan damben ta ko ina babu masaka tsinke don bawa idon su abinci.

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button