Wasanni

Ana Zargin Ma’aikacin Bankin UBA ya Saci N3,390,000 Daga Asusun Kwastoma a Kano

Ana zargin ma’aikacin banki ya saci N3,390,000 daga asusun kwastoma a bankin United Bank Of Africa UBA dake Sharaɗa a jihar kano

Garzali Wada Ibrahim yace ya kai ƙorafi bankin domin a seta masa manhajar da ake amfani da ita don tura kuɗi inda ya haɗu da wani ma’aikacin banki mai suna Osaka Omada dake ɓangaren kula da kwastamomi wanda ya sake saita mushi manhaja ta wayar salula wato mobile application.

Ibrahim ya ƙara da Cewa a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2023. An cire wasu kuɗaɗe ba tare da izinin sa ba daga cikin Asusunsa har naira miliyan uku da dubu ɗari uku da casa’in (N 3,390,000) ta wannan manhaja dake wayar sa.

“Bayan an cire ne sai nayi mamaki kuma nayi zargin Osaka Omada na UBA din Sharaɗa ne da yin wannan aika-aika domin babu wanda yaga lambobin sirrin cire kuɗi daga manhaja ta face Osaka domin yana kallo na saka.” inji Garzali

Kashi na farko na kudaden da aka sata sun kai kimanin 2,000,000 inda aka tura su zuwa asusun bankin Wema mai lamba 7790847364 mai dauke da sunan BSTPOS-Musa.

Haka zalika kashi Na biyu na kuɗin da aka cire ya kai kimanin 1.300.000 inda aka tura shi zuwa asusun Opay mai lamba 9068129712 mai suna Angela Anulika weke

Ya ƙara da cewa yayi yunƙurin neman haƙƙin sa domin a dawo masa da kuɗaɗen sa amma haƙan sa yaci tura saboda haka ya buƙaci Babban Bankin Najeriya ya shiga tsakanin sa da Bankin United Bank Of Africa UBA rashen Sharaɗa dake jihar kano.

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button