Wasanni

Yadda Ake Bude JAMB Profile

YADDA AKE BUƊE JAMB PROFILE

Mallakar Profile Codes shi ne matakin farko, kuma ginshiƙi a fannin rijistar jarrabawar JAMB UTME ko DE. Domin da Profile Codes ne ake iya sayen lambobin rijistar jarrabawar UTME, ko tsarin shiga Jami’a kaitsaye na DE (ePIN).

Domin sauƙaƙa tsarin, hukumar JAMB ta bada damar buɗe Profile, tare da mallakar lambobin na Profile Codes ta hanyar aikewa da saƙonnin kar ta kwana (Messages), a wayoyin salula.

GA YADDA MATAKAN BUƊE PROFILES ƊIN SU KE :

  • Ku shiga wurin rubuta saƙon Messages na wayoyinku, sai ku rubuta NIN, ku bada tazara (Space), Sannan ku rubuta lambobin katin ɗan ƙasarku a gaba.

Misali: NIN 1234567890

  • Sai ku aike da saƙon zuwa lambar, 55019 ko 66019.

Daga nan za ku samu saƙo ɗauke da cikakkun sunayenku, tare da lambobin Profiles Codes da JAMB ta samar muku, wanda da su ne za ku yi amfani wajen sayen ePIN.

KU SANI: Wajibi ne ya kasance akwai kuɗin da bai gaza Naira 50 ba, akan layukan da za ku yi amfani da su wajen aikewa da wannan saƙo, domin kuwa JAMB na ɗaukar Naira 50 ne, kafin Aiko muku da lambobin.

GA MASU TAMBAYA, KO SON SHIGA ASOF JAMB GROUP, ZA SU IYA AIKE MANA DA SAƘONNI A WHATSAPP, TA WANNAN LAMBAR: 08039411956.

Rubutawa: Miftahu Ahmad Panda.

08039411956

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button