Wasanni
Muhimman Batutuwa Game Da JAMB UTME Da DE
MUHIMMAN BATUTUWA KAN JAMB UTME DA DE NA SHEKARAR 2024

- Ana tsaka da Generating ɗin JAMB Profile, domin mallakar Profile Codes, a yanzu haka.
- Za a fara rijistar JAMB UTME a ranar Litinin 15 ga watan Janairu, za kuma a rufe a ranar 26 ga watan Fabrairun 2024.
- Kuɗin rijistar JAMB UTME Naira 6,200 ne (Idan ba za a yi Mock ba, Idan kuma har da jarrabawar gwaji ta Mock kuma Naira 7,700).
- Za a fara rijistar DE, a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, za a rufe a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris ɗin 2024.
- Za a rubuta jarrabawar gwaji ta Mock, a ranar 7 ta watan Maris.
- Za a fara cire JAMB UTME Slip, a ranar 10 ga watan Afrilun 2024.
- Za a rubuta jarrabawar JAMB UTME, daga ranar Juma’a, 19 ga watan Afrilu, zuwa Litinin, 29 ga watan Afrilun 2024
DOMIN TAMBAYA, KO SHIGA ASOF JAMB GROUP, KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR: 08039411956.
✍️ MIFTAHU AHMAD PANDA
08039411956