Cikakken Bayani Game Da Jarrabawar Mock
Mock jarrabawace da hukumar JAMB ta ke shiryawa, ga ɗaliban da su ka nuna sha’awa, domin auna fahimta da ingancin shirin da su ka yi na tunkarar babbar jarrabawar UTME.

Akan rubuta Mock ne kuma a matsayin gwaji, kafin lokacin rubuta JAMB UTME ta ainahi, saboda haka ba wajibi ba ne ga dukkannin ɗaliban da za su rubuta jarrabawar JAMB UTME su rubuta ta, domin akan shiryata ne, ga ɗaliban da su ka nuna sha’awa kaɗai.
Ana kuma rubuta jarrabawar Mock ne, ta hanyar amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer), haka zalika tana da tambayoyi kwatankwacin na jarrabawar JAMB UTME.
ALFANUN RUBUTA JARRABAWAR MOCK:
- Mock na tallafa wa Ɗalibi wajen fahimtar nagartar shirin da ya yi, ta fuskar karatu, domin tunkarar jarrabawar JAMB UTME, duba da yadda tambayoyin MOCK ɗin su ke kamanceceniya da na UTME.
- Haka zalika, MOCK na taimaka wa Ɗalibi wajen naƙaltar salon da hukumar JAMB ta ke bi, domin shirya tambayoyinta, tun kafin tsintar kansa a ɗakin rubuta jarrabawar ta zahiri.
•Mock, na taimaka wa Ɗaliban da ke da ƙarancin ƙwarewa ta fuskar amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer), wajen fahimtar ko za su iya amfani da Computer, a ya yin jarrabawar JAMB UTME ta zahiri ? (Idan Ɗalibi, ya ga ya yi Mock lafiya ƙalau a Computer, ba tare da fuskantar wani ƙalubale ba, to hakan ya na nufin zai iya amfani da ita a lokacin JAMB UTME lafiya ƙalau; ya yin da ganin akasin hakan kuma ya ke nuna buƙatar zuwa neman horo akan yadda ake amfani da Computer, domin rubuta jarrabawar JAMB).
SAURAN BATUTUWA GAME DA MOCK:
√• Ɗalibin da ke da sha’awar rubuta jarrabawar Mock, zai bayyana sha’awarsa ta rubuta jarrabawar ne, ya yin da ake masa rijistar UTME, a JAMB CBT Centre.
√• Ana biyan ƙarin Naira 1,500 akan kuɗin rijistar JAMB UTME, domin rubuta jarrabawar (wanda ba zai yi MOCK ba, zai biya Naira 6,200; wanda zai yi MOCK zai biya Naira 7,700).
√• Ita ma ana cire Slip ɗinta ne, ya yin da ake daf! da rubuta jarrabawar, kamar yadda ake a JAMB UTME.
√• Ba a amfani da makinta wajen samun Admission, kawai makin ya na nuna irin ƙwazon Ɗalibi, da shirinsa wajen tunkarar JAMB UTME ne.
DOMIN TAMBAYA KO NEMAN SHIGA ASOF 2024 JAMB GROUP, KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR: 08039411956.
Rubutawa: Miftahu Ahmad Panda.
08039411956