Wasanni

Bayani Akan Direct Entry

Direct Entry, ko DE a taƙaice, tsari ne na shiga Jami’a kaitsaye, ba tare da rubuta jarrabawa ba (a baya), da hukumar JAMB ta ɓullo da shi, kuma waɗanda su ka samu zarafin shiga Jami’a ta wannan tsarin, su kan fara karatunsu na Digirin farko ne daga aji biyu (Level 200).

Ɗaliban da ke da damar neman guraben karatu (Admissions), a Jami’o’i ta wannan tsarin su ne Ɗaliban da su ka kammala Karatun Diploma (ND); Karatun Ƙwarewa a harkar Malanta (NCE); IJMB; har ma da masu Babbar Diploma ta ƙasa (HND) da ke son ɗaga likkafar karatunsu zuwa matakin Digiri (masu HND su na farawa daga Level 300).

Sai dai, daga zangon karatu na 2024/2025 masu neman shiga Jami’o’in Najeriya ta wannan tsari na DE, su ma dole ne su rubuta jarrabawa, amma ba irin ta masu UTME ba, domin kuwa hukumar JAMB ta damƙa wuƙa da nama ga Jami’o’i wajen shirya jarrabawar tantancewa ga Ɗaliban DE ɗin, da su ka nemi guraben karatu, a Jami’o’insu, kuma shirin zai fara ne, daga wannan shekarar (jarrabawar za ta iya kasancewa a rubuce, ko kuma baki da baki).

√• WANNE IRIN MAKI NA KE BUƘATA A SAKAMAKONA, DOMIN NEMAN JAMI’A TA HANYAR DE ?

Kamar yadda, babu wani maki na bai ɗaya da Jami’o’i su ke amfani da shi wajen bayar da guraben karatu, ga Ɗaliban da su ka neme su ta hanyar jarrabawar JAMB UTME (kowacce makaranta ita ke fitar da makin da ta ke buƙata), to haka ma a tsarin DE, abin da kowacce Jami’a ke buƙata, daga Ɗaliban da ke neman makarantar ya sha ban-ban, Misali: ya yin da Jami’ar Bayero (BUK) ta ce wajibi ne wanda za ta bawa Admission ta hanyar DE ya kasance ya na da Upper Credit – toh! Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) za ta iya cewa har masu Lower Credits su zo, za ta basu Admissions. A taƙaice dai, abin da Jami’o’in ke buƙata ya na ban-banta ne, kwatankwacin yawan Ɗaliban da ke nemansu (Competition Rate).

å SHIN A KOWACCE MAKANTA NA YI KARATU, ZAN IYA CIKE DE ?

Wannan tambaya, amsarta na zuwa da ‘Eh’ da ‘A’a’ a lokaci guda, domin kuwa kowanne Ɗalibi da ya kammala guda daga cikin matakan karatun da mu ka ambata a sama, ya na iya cike DE, sai dai wasu matsaloli na iya zamewa Ɗaliban tasgaro.

Ga wasu daga ciki:

  • Rashin Samun JAMB Admission a lokacin da aka fara karatun ND ko NCE – Neman Jami’a ta hanyar DE, na zamewa da dama daga cikin ɗaliban da su ka kammala makarantun gaba da Sakandire ‘Ɗan Zani’, sakamakon gaza samun Admission ɗin JAMB a lokacin da su ke karatu, a makarantun da su ka kammala. Domin kuwa yadda abin ya ke a dokar Ilimin Najeriya shi ne: wajibi ne sai Ɗalibi ya samu Admission ɗin JAMB a kowanne irin karatu zai yi, amma rashin girmama wannan mataki ya sanya da dama daga cikin Kwalejojin Lafiya, Da Wasu Daga Cikin Makarantun Kuɗi, su ke bada Admissions ɗin, ba tare da amfani da JAMB ba, wanda daga bisani hakan ke zamewa Ɗaliban tasgaro, a hanyarsu ta tsallakawa zuwa makarantun gaba (musamman Jami’o’i).
  • Rashin tantance Makaranta, Ko Darasin Da Ɗalibi Ya Karanta – Ɗalibai da dama, su kan gaza samun guraben karatu (ko da kuwa sun samu damar cike DE), sakamakon rashin samun cikakkiyar tantancewa ta kwas ɗin da su karanta, a makarantun da su ka kammala.

å SHIN ANA IYA CIKE DE AWAITING RESULT ?

Daga shekarar da ta gabata, hukumar JAMB ta tsame Ɗaliban da ke neman Jami’a kaitsaye (DE), daga cikin jerin Ɗaliban da za su cigaba da amfana da tsarin jiran samako (awaiting result), tare da sanya tsatstsauran mataki akan tsarin, bayan da ta zargi da yawa daga cikin Ɗalibai, da yin amfani da sakamakon kammala manyan makarantu na bogi (fake results). A taƙaice dai wajibi ne ga dukkannin wanda ke son neman Jami’a ta hanyar DE, ya kasance ya na da sakamakonsa na kammala ND, NCE ko IJMB a hannu.

å A INA AKE RIJISTAR DE ?

A shekarun baya, ana rijistar DE ne, a kowacce daga cikin Cibiyoyin Rijistar JAMB, da hukuma ta amince da su (Approved CBT Centres), amma a yanzu tsarin ya sauya, domin kuwa ana iya rijistar DE ne, a Ofisoshin hukumar JAMB, na jihohi kawai (JAMB State Offices).

√• DA ME – DA ME AKE ZUWA WURIN RIJISTAR DE ?

  • Sakamakon Kammala Makarantar Gaba Da Sakandire (ND, NCE & IJMB).
  • Sakamakon Kammala Makarantar Sakandire (NECO, WAEC, NABTEB & NBAIS).
  • Profile Codes.
  • Kuɗin Rijista (Naira 6,200).

KU TABBATAR KU NA DA JAMB NUMBER; ADMISSION ƊIN JAMB; TARE DA SAKAMAKON ƘARSHE NA MAKARANTUN DA KU KA KAMMALA, KAFIN YUNƘURIN CIKE DE FORM.

Domin Tambaya: 08039411956 (WhatsApp).

Rubutawa: Miftahu Ahmad Panda.

08039411956

Unity Online Hausa

Domin samu labarai da suka shafi Duniya, Wasanni, nishadi, kasuwanci, Siyasa, kimiyya,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button